in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana kokarin magance ta'addanci daga tushe
2019-01-18 14:51:33 cri

A kwanakin baya, wasu sanannun 'yan jaridun kasashen dake kan hanyar siliki, sun ziyarci cibiyar koyar da ilimin sana'a ta musamman ta birnin Kashgar dake kudancin yankin Xinjiang na kasar Sin, inda 'yan jaridu daga kasashen Turkiya, Masar, Afghanistan, Pakistan, Bangladesh da Sri Lanka suka yi mu'amala tare da masu karatu da malamai a cibiyar.

Bisa fasahohin da aka samu yayin da ake yin yaki da ta'addanci a ciki da waje, masu tsattsauran ra'ayi za su haifar da ra'ayin ta'addanci. Idan ana son kawar da ta'addanci, ya kamata a kawar da tunanin ra'ayin daga tushe.

Yankin Xinjiang yana gudanar da ayyukan yaki da ta'addanci, tare da magance ta'addanci gaba daya, wanda ya hada da aikin yaki da ta'addanci, da tabbatar da hakkin dan Adam, wata muhimmiyar hanya da ake yi amfani da ita ita ce kafa cibiyar koyar da ilimi na sana'a ta musamman, inda ake horar da mutanen da ra'ayin ta'addaci da tsattauran ra'ayi suka yi musu tasiri sosai, wadanda laifinsu ba su da tsanani, ko kuma wadanda aka soke yanke hukunci gare su.

Cibiyar koyar da ilimin sana'a ta musamman dake birnin Kashagar ta horar da mutane da ilmin koyon Sinanci, da dokoki da fasahohi don kawar da tsattsauran ra'ayi. Kana cibiyar ta samar da abinci da wurin zaune, da samar da ayyukan yi ga mutanen da suka samu gama karatu a cibiyar.

Ajin cibiyar yana da kyau, an sanya kalmomi kamar "Yin rayuwa cikin kyawawan halaye" da "za a samu kyakkyawar makoma" da wasu zane-zanen da masu karatu a cibiyar suka yi a kan bangon ajin. Malamai sun yi amfani da yaren Uygur da Sinanci wajen samar da ilmi, a sa'i daya kuma, yawancin masu karatu suna iya yin amfani da Sinanci.

Shugaban kungiyar 'yan jaridu ta Izmir ta kasar Turkiya Misket Dikmen ya bayyana cewa, a matsayin wani dan jarida, yana da babbar ma'ana ne wajen kai ziyara a cibiyar koyar da ilimin sana'a ta musamman. Ya bayyana cewa,

"Akwai ra'ayoyi da dama game da cibiyar koyar da ilimin sana'a ta musamman din, daya daga cikinsu shi ne kawar da alamun kabilu daban daban, da mai da su kamar kabila daya. Amma a ganina, wannan babbar makaranta ce, mutanen dake karatu a cibiyar suna kokarin kawar da tunani maras dacewa, da ba da ilmi. Sun gaya mini da kansu cewa, sun zo cibiyar koyon fasahohi bisa radin kan su, wannan zabi ya maye gurbin yanke hukunci gare su. Don haka, sun koyi ilmi da fasahohi don samun karfin yin rayuwa a nan gaba. Dukkan masu karatun da na yi hira da su, sun nuna gamsuwa da halin rayuwarsu na yanzu, da yanayin karatu a cibiyar."

A yayin ziyarar, 'yan jaridu na kasashen shida sun yi mu'amala tare da masu karatu a cibiyar sosai. Babban direktan jaridar Kandahar Orband ta kasar Afghanistan Abdul Matin Amiri ya bayyana cewa,  

"Kafin hakan, na samu wasu labaru cewar gwamnatin kasar Sin ta yi garkuwa da wasu mutane ta karfin tuwo, da 'yan sandan kasar Sin sun tilasta musu shiga horaswa na koyon fasahohi, har ma an tsare su a kurkuku. Amma a halin yanzu, na gani da idona a nan, ba aikin tilastawa ba ne, wannan makaranta ce kawai. Na yi hira da wasu masu karatu a nan, suna farin ciki a nan, abu mafi muhimmanci shi ne sun koyi ilmi da fasahohi. Abin da ya fi burge ni shi ne, an kawar da tsattsauran ra'ayinsu daga tushe, an daidaita matsalarsu."

'Dan jarida na ATV na kasar Turkiya Erdal Kurucay ya bayyana cewa,  

"A da, na samu labaru daga kafofin watsa labaru na yammacin kasashen duniya, domin tabbatar da matsayina bisa labarinsu, wannan a ganina kuskure ne. Bayan da na ziyarci cibiyar koyar da ilimin sana'a ta musamman, na canja ra'ayina. A hakika sun aikata laifi, domin tsattsauran ra'ayi ya yi tasiri gare su. Cibiyar koyar da ilimin sana'a cibiya ce ta samar da ilmi. Masu karatu sun koyi ilmi da fasahohi, don daga darajarsu a zamantakewar al'umma. Kana aikin cibiyar shi ne kyautata halayensu, wadanda za su kawar da ra'ayinsu maras dacewa, da sake inganta zamantakewar al'umma. Dukkan mutanen sun yi kuskure, abu mafi muhimmanci shi ne a gano kuskure da gyara shi."

A ajin koyon kide-kide, masu karatu sun sanya tufaffin kabilu da buga kayan kide-kide na kabilunsu, da mata da maza suna rera waka da yin raye-raye, da shaida fasahohinsu. A filin wasa, masu karatu suna buga wasan kwallon kwando da kwallon raga, da kwallon tebur da sauransu. A wurin cin abinci, masu karatu sun ci abinci da yin hira da 'yan jaridu, da gayyace su da cin abinci tare. Dukkan masu karatu sun ji dadi, sun more rayuwarsu a cibiyar. Mai jagoran shiri na gidan rediyon sada zumunta a tsakanin Sin da Pakistan FM98 na kasar Pakistan Tassawar Zaman Babar ya bayyana cewa,

"Bayan da na ziyarci cibiyar, na jinjinawa kasar Sin bisa kokari ta na kawar da tsattsauran ra'ayi. Makasudin kafa cibiyar shi ne kara yin mu'amala a tsakanin jama'a, da zama tare cikin lumana, da nuna girmama juna, ta hanyar samar da ilmi da fasahohi gare su, da kawar da tsattsauran ra'ayi, da kau da nuna kiyayya ga kasa, da jama'a, da kabila."

Mai tsara shiri na jaridar Daily Sun ta kasar Bangladesh Shiabur Rahman ya bayyana cewa,  

"Ban da koyar musu da ilimin dokoki, da yadda za a yi ayyuka masu dacewa, abu mafi muhimmanci shi ne a koyar musu da fasahohi, ta hakan za su iya yin amfani da su, da yin rayuwa a zamantakewar al'umma yadda ya kamata, da samar musu da kyakkyawan fata da imani, sannu a hankali za su koma zaman rayuwa mai dacewa yadda ya kamata."

Yaki da ta'addanci da kawar da tsattauran ra'ayi su ne manyan matsalolin duniya. 'Yan jaridun sun bayyana cewa, yankin Xinjiang ta kafa cibiyar kamar hakan, wanda ya samar da gudummawa ga duniya wajen daidaita wannan matsala ta wannan tsarin kasar Sin, ya kamata kasa da kasa su koyi fasahohi daga wannan batu. Babban direktan jaridar Kandahar Orband ta kasar Afghanistan Abdul Matin Amiri ya bayyana cewa,

"Kasar Afghanistan ta kan gamu da hare-haren ta'addanci, idan kasar Afghanistan ta koyi fasahohin kasar Sin, da kafa cibiya kamar wannan, na yi imani cewa, za a canja ra'ayin masu kaddamar da hare-haren ta'addanci a nan gaba."

Direktan mujallar Al-Ahram Ektassdy ta kasar Masar Samia Fakhry Mansour ya bayyana cewa,

"Wannan aiki yana da kyau, ya kamata sauran kasashen duniya su koyi fasahohi daga wannan aiki, musamman ga mutanen da tsattsauran ra'ayi ya yi tasiri gare su, ana iya ceton su da kawar da tsattsaura ra'ayi daga gare su cikin hanzari." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China