in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira ga Amurka da ta daina yunkurin dakile kamfanonin sadarwar ta
2019-01-18 10:40:10 cri
A jiya Alhamis ne kasar Sin, ta yi kira ga 'yan majalisun dokokin Amurka da su daina yunkurin samar da dokoki, wadanda za su baiwa kasar damar dakile ayyukan kamfanonin sadarwa na Sin ciki hadda Huawei da ZTE da sauran su. Kasar Sin ta kuma yi tir da matakan danniya a fannin hada hadar fitar da kayayyaki zuwa Amurka.

Da take tsokaci game da hakan, yayin taron manema labarai na jiya Alhamis, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Hua Chunying, ta ce wasu 'yan majalissar dokokin Amurka na gabatar da kudurin dokoki, da nufin shatile kamfanonin sadarwa na Sin. Ta ce hakan na nuna tsananin ji da kai, da kuma rashin karfin gwiwar su na fuskantar gaskiya.

Uwar gida Hua ta kara da cewa, abu ne a fili cewa, burin Amurka shi ne yin amfani da duk wata kafa ta karfin iko, wajen gurgunta ayyukan fasahohi na kasar Sin. Don haka a cewar ta, Sin na adawa da keta hurumin kamfanoninta ta hanyar fakewa da matakan kula da shigar da hajoji Amurka.

Daga nan sai ta yi kira ga 'yan majalisun dokokin Amurka, da su dakatar da yunkurin murkushe kamfanonin Sin, su kuma dakatar da kafa irin wadannan dokoki masu illa, kana su himmatu wajen gina matakan amincewa da juna, da hadin gwiwa tsakanin Sin da tsagin Amurka.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China