in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MOC: Sin tana fata cigaban fasaharta ya amfanawa duniya baki daya
2019-01-18 10:37:03 cri
Ma'aikatar cinikin kasar Sin (MOC) ta sanar a jiya Alhamis cewa, fasahar kirkire kirkirenta da cigabanta ba zai iya zama barazana ba ga duniya, kuma kasar Sin tana fatan cigaban fasahar data samu ya amfanawa duniya baki daya.

Kakakin ma'aikatar cinikin ta MOC, Gao Feng, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a lokacin da yake karin haske game da matakan da wasu kasashen yammacin duniya suka dauka na kin saya ko kuma takaita sayan kayayyakin fasahar kasar Sin.

Maganganun da ake na nuna fargaba da barazanar tsaro game da kamfanonin kasar Sin da kayayyakin kasar kazafi ne ake yadawa, in ji Gao. "Zargin da ake yi game da barazanar fasahohin kasar Sin ga duniya jita-jita ne maras tushe balle makama."

"Wasu kasashen duniya, musamman wadanda suka cigaba ta fuskar tattalin arziki, ya kamata su rungumi amfani da kayayyakin manyan fasahohin sauran kasashe da suka hada da kasar Sin, da zuciya daya domin biyan muradin al'ummominsu na cikin gida," in ji shi.

Gao ya ce ma'aikatar zata cigaba da nuna goyon baya ga kamfanonin kasar Sin karkashin hadin gwiwar cin moriyar juna a tsakanin kasa da kasa don bunaksa cigaban fasahohi da cinikayya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China