"Bisa la'akari da ma'aikatan Amurka 800,000 da ba su samu albashinsu ba kuma domin tabbatar da ganin tawagarsa ta taimaka kamar yadda aka bukata, shugaba Trump ya soke tawagar kasarsa a taron tattalin arziki na duniya a Davos, na kasar Switzerland," inji kakakin fadar ta White House Sarah Sanders.
An dauki matakin soke ziyarar ta kasar Swiss ski ne tun a makon jiya sakamakon takaitaccen rufewar ma'aikatun gwamnatin Amurka kuma an umarci wakilan Amurkan, wanda sakataren kudin Amurkan Steven Mnuchin ke jagoranta, da su halari wani taron dandali na shekara shekara a madadin zuwa Davos din. (Ahmad Fagam)