Rahoton yana tsammani cewa, ana fuskantar kalubale da dama a halin yanzu bayan da aka fuskanci matsalar raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da rashin daidaici kan tattalin arziki, da sauyin yanayi, da matsalar siyasa a kan iyakar kasa, da kwaskwarima kan masana'antu karo na 4 da sauransu.
Shugaban dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya Borge Brende ya bayyana cewa, bisa hadarin da za a fuskanta a fannin cinikin duniya da bunkasuwar tattalin arziki a shekarar 2019, ya kamata kasa da kasa su kara yin hadin gwiwa da juna. Ana bukatar kasa da kasa su cimma daidaito da yin kokari tare don kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Zainab)