in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi garkuwa da dan kasar Canada a Burkina Faso
2019-01-17 09:48:21 cri
A jiya Laraba tashar talabijin ta CTV ta bada rahoton cewa an yi garkuwa da wani dan kasar Canada a kasar Burkina Faso dake yammacin Afrika a daren ranar Talatar da ta gabata.

Mutumin mai suna Kirk Woodman, wasu 'yan bindiga ne suka yi garkuwa da shi a wajen wani kamfanin hakar ma'adanai mallakar wani dan asalin kasar Canadan a kusa da kan iyakar Burkina Faso da Nijer, in ji tashar ta CTV.

Ministar harkokin wajen kasar Canada Chrystia Freeland ta ce, jami'an kasar Canadan sun samu rahoton kuma suna ci gaba da tuntubar iyalan mutumin.

An yi garkuwa da mutumin ne bayan da wata mace 'yar asalin kasar Canadan mai shekaru 34 da haihuwa Edith Blais da abokinta dan kasar Italiya Luca Tacchetto aka bada rahoton bacewarsu a lokacin da suke bulaguro tare a kasar ta yammacin Afrika a farkon wannan wata.

Burkina Faso ta kafa dokar ta baci a lardunanta dake arewacin kasar tun daga ranar 31 ga watan Disambar shekarar da ta gabata, bayan wani harin mayaka masu da'awar yin jihadi a kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China