Madam Hua ta bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa kan tambayar da aka yi mata game da shirin Burtaniyar na ficewa daga EU.
A jiya ne 'yan majalisar dokokin kasar ta Burtaniya suka kada kuri'un kin amincewa da babban rinjaye kan yarjejeniyar ficewar kasar daga kungiyar ta EU. Mambobi 202 ne suka kada kuri'ar amince da yarjejeniyar yayin da 432 kuma suka kada kuri'ar kin amincewa da yarjejeniyar da gwamnatin Burtaniya da kungiyar ta EU suka amince.
Madam Hua ta ce, kasar Sin tana dora muhimmanci kan shirin ficewar Burtaniyar daga EU, tana kuma sane da wasu 'yan bambance-bambance a kasar da ma tsakanin Burtaniya da kungiyar EUn game da ficewar kasar daga kungiyar.
Ta ce, manufar kasar Sin game da bunkasa alaka tsakanin Sin da Burtaniya da kuma Sin da EU ba za ta canja ba. (Ibrahim)