Rahoton ya nuna cewa, tun da kasar Sin ta zama mambar kungiyar ciniki ta duniya WTO a shekarar 2001, tattalin arzikin ta, da na sauran kasashen dake yankin Asiya da tekun Pasific ke kara hadewa waje guda, kana kowanensu na dogaro kan cinikayyar da ake yi tsakaninsu matuka.
Yanzu haka da yawa daga cikin kasashen dake yankin Asiya da tekun Pasific suna fitar da mafi yawan kayayyakinsu zuwa kasar Sin, kana sun fi shigo da kayayyaki daga kasar Sin, idan an kwatanta da na sauran kasashe.
An ce, ko da yake saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya dan ragu, amma ana ci gaba da hasashen ganin kasar ta kasance wuri mafi muhimmanci da sauran kasashen dake yankin Asiya da tekun Pasific suke fitar da kayayyakinsu. Saboda yadda ake kokarin shiga tsarin samar da kayayyaki na yankin Asiya, da neman tura kaya zuwa kasuwannin kasar Sin, ita ce manufa mai muhimmanci ga yawancin kasashen dake yankin Asiya da tekun Pasific, a kokarinsu na raya masana'antu. (Bello Wang)