An gudanar da bikin ne a fadar shugabancin kasar, inda mambobin gwamnatin 38 suka yi rantsuwar kama aiki. Bayan haka, sabon firaministan kasar Julien Bekale, ya bayyana wa kafofin watsa labaru cewa, yadda shugaba Bongo ya halarta, da kuma jigorantar bikin, ya karyata jita-jitar da aka yada, cewa lafiyar jikinsa ta tabarbare.
An ce shugaban ya koma gida a daren ranar 14 ga wata, sai dai ba a bayyana ko zai sake komawa jinya a kasashen waje ba.
Ali Bongo ya dade yana samun jinya a ketare, tun daga watan Oktoban bara. Kana an ga fuskarsa a baya bayan nan ne a jawabin sa na taya muryar sabuwar shekara da ya gabatar wa jama'ar kasarsa, ta wani bidiyon da aka dauka.
A ranar 7 ga watan nan, an yi yunkurin wani juyin mulki a Libreville, fadar mulkin kasar, wanda bai samu nasara ba, inda sojoji masu ta da kayar baya suka ce Ali Bango, ba zai iya ci gaba da mulki ba sakamakon tabarbarewar lafiyar jikinsa. (Bello Wang)