in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta kaddamar da hari a kauyukan jihar Borno
2019-01-16 09:49:14 cri
A Najeriya mayakan kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram, sun kaddamar da hare-hare a kauyuka biyu dake kusa da birnin Maidugurin jihar Borno.

Rahotanni sun ce maharan sun farwa kauyen Rann mai nisan sama da kilomita 170 daga birnin Maiduguri da yammacin Litinin. Kaza lika wasu mayakan kungiyar sun farwa kauyen Damasak.

A kuyen Rann, mayakan kungiyar sun kone asibiti, da makaranta, da sauran gine-ginen gwamnati. Sun kuma yi yunkurin karbe sansanin sojojin gwamnati dake wurin. An ce an yi dauki ba dadi tsakaninsu da sojojin, kafin daga karshe sojojin su fatattake su

Rundunar sojojin kasar dai ba ta fitar da sanarwa a hukumance game da harin ba tukuna. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China