in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin mutanen da suka ji raunuka sakamakon harin boma-bomai a Afghanistan ya haura zuwa 113
2019-01-15 20:40:00 cri
Rahotanni daga kafofin watsa labaran Afghanistan sun ruwaito cewa, harin boma-boman da aka kai a yankin 'yan sanda na tara dake Kabul, fadar mulkin kasar, a daren jiya Litinin, ya hallaka mutane hudu, tare da raunata wasu 113.

Kungiyar Taliban ta kasar ta sanar da daukar alhakin kai harin a yau Talata, inda ta ce, dakarunta guda biyar sun kai harin ne kan wani matsugunin baki 'yan kasashen waje dake unguwar Green Village ta yankin 'yan sanda na tara dake Kabul, inda a cewarta, ya hallaka 'yan kasashen waje akalla goma.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China