Xu Hongcai ya yi bayani cewa, kara karfin yana nufin kara karfin rage harajin kaya da kara zuba jari. Za a kara rage harajin kaya don sassauta matsin lambar da sha'anin kera kayayyaki, da kamfanoni kanana suke fuskanta, tare da nuna goyon baya gare su. Kana, za a kara zuba jari bisa yanayin tattalin arziki da bukatun fannoni daban daban.
Wannan jami'in ya kara da cewa, kara tabbatar da inganci yana nufin kara yin amfani da tsarin kudi, da yadda za a yi amfani da kudi. Za a maida hankali ga manyan fannoni, kamar su yaki da talauci, da noma, manoma da kauyuka, da yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, da kiyaye muhalli, da kyautata zaman rayuwar jama'a da sauransu. (Zainab)