in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Turkiya da Amurka sun buga waya ga juna don tattauna batun Syria
2019-01-15 10:37:54 cri
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdoğan, da shugaban kasar Amurka Donald Trump, sun zanta ta wayar tarho a jiya 14 ga wata, don tattauna batun kasar Syria.

A cikin sanarwar da fadar shugaban kasar Turkiya ta bayar a wannan rana, Erdoğan da Trump sun jaddada cewa, ya kamata a aiwatar da taswirar hadin gwiwa ta Manbj, don hana fuskantar yanayin rashin samun shugabancin yankin, bayan da kasar Amurka ta janye sojoji daga yankin, da kuma kawar da cikas na janyewar sojojin kasar Amurka. Kana bangarorin biyu sun tatauna, da kafa wani yankin kiyaye maras dakaru a ciki a arewacin kasar Syria, bisa tushen tabbatar da ikon mallakar kasar Syria.

Sanarwar ta kara da cewa, Erdoğan ya jaddada cewa, babu matsala tsakanin Turkiya da Kurdawa dake kasar Syria, kuma burin kasar Turkiya shi ne murkushe kungiyar IS, da jam'iyyar kwadago ta Kurdawa ko PKK da reshenta.

Kakakin fadar shugaban kasar Amurka Sarah Sanders ta bayyana a cikin sanarwar da aka gabatar a wannan rana cewa, shugaba Trump ya bayyana fatansa, na yin hadin gwiwa tare da kasar Turkiya, don warware matsalar tsaro game da yankin arewa maso gabashin kasar Syria, kana ya jaddada cewa, tabbatar da tsaron dakarun Kurdawa yana da muhimmanci ga kasar Amurka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China