in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya gana da mai jiran gadon sarautar hadaddiyar daular Larabawa a birnin Abu Dhabi
2019-01-15 09:58:58 cri
Jiya Litinin, wakilin musamman na shugaban kasar Sin, kana mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar JKS Yang Jiechi, ya gana da mai jiran gadon masarautar hadaddiyar daular Larabawa Mohammed bin Zayed Al Nahyan a birnin Abu Dhabi.

A yayin ganawar tasu, Yang Jiechi ya bayyana cewa, cikin shekarar 2018, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki mai ma'ana kwarai a kasar masarautar hadaddiyar daular Larabawa, kuma babban makasudin ziyarar tasa a wannan karo shi ne, aiwatar da ra'ayi daya da shugaba Xi, da mai jiran gadon sarautar suka cimma. Ya ce a halin yanzu, kasashen biyu suna gudanar da shirye-shiryen hadin gwiwa bisa shirin "Ziri daya da hanya daya" cikin yanayi mai kyau, kuma a nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da masarautar hadaddiyar daular Larabawa, domin samun karin sakamako masu kyau, ta yadda za a tallafawa al'ummomin kasashen biyu.

A nasa bangare kuma, Mohammed bin Zayed Al Nahyan, ya ce kasarsa tana son yin hadin gwiwa da kasar Sin, wajen aiwatar da ra'ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kuma karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban, bisa shirin "Ziri daya da hanya daya". Haka kuma, tana son kara fadada mu'amala tsakanin kasashen biyu, kan harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, domin inganta dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare.

Bugu da kari, ya ce, hadaddiyar daular Labarawa tana goyon bayan kasar Sin kan matakan da ta dauka wajen yaki ta ta'addanci, kuma tana fatan karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu kan wannan aiki, domin tabbatar da zaman lafiya da zaman karko a yankin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China