in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNCTAD: Sin na sahun gaba a cinikayyar hajojin fasahohi da sana'o'in nuna basira
2019-01-15 09:41:09 cri

Wani rahoto na MDD da aka fitar a jiya Litinin ya nuna cewa, kasar Sin na sahun gaba a fannin cinikayyar hajojin fasahohi, da na nuna basirar bil Adama, yayin da hada hadar fitar da kayayyaki daga wannan sashe na cinikayya ke fadada, da sama da kaso 7 bisa dari. Rahoton ya ce kasar Sin ta zamo ta daya a duniya bisa alkaluman cinikayyar wannan sashe.

Rahoton na taron karawa juna sani na MDD game da hada hadar cinikayya da samar da ci gaba ko UNCTAD, na kunshe da bayanai game da kasashe masu karfi da masu tasowa 130, ya kuma gabatar da jadawalin ci gaba na kasashen, ta fuskar bunkasar fannin cinikayyar hajojin fasahohi da na nuna basirar bil Adama.

Cikin wannan jadawali, Sin na dauke da sama da kaso daya bisa uku na hajojin da ake sayarwa, ko ake yin gwanjon su. Kaza lika ta yi fice wajen shirya fina finai dake tashe a duniya, baya ga rawar gani da take takawa a kasuwannin kasa da kasa na kera kayan katako, da tufafi, da kayan ado.

UNCTAD ya ce a shekarar 2002, darajar hada hadar cinikayya ta Sin a wannan fanni, ta kai dalar Amurka biliyan 32. Ya zuwa shekarar 2014, wannan adadi ya karu da sama da rubi biyar, wanda ya kai ga darajar kudi har dala biliyan 191.4.

Bugu da kari, yayin wani taron manema labarai da ya gudana lokacin taron karawa juna sanin na MDD, an fitar da wata sanarwa dake nuna cewa, cinikayyar kayayyakin fasahohin nuna basira na kasa da kasa na kara fafada, inda Sin ta zamo kasuwa mafi girma a wannan sashe.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China