in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar 'yan wasan kwallon kafa mata ta Najeriya ta tashi zuwa Sin
2019-01-15 09:23:56 cri

Tawagar mata 'yan wasan kwallon kafa ta Najeriya, ta tashi daga kasar zuwa kasar Sin, domin halartar gasar kasashe 4, tare da share fagen buga gasar cin kofin duniya ta hukumar FIFA karo na 8 da za a yi a kasar Faransa.

Wata sanarwa da hukumar kwallon kafar kasar ta fitar, ta ce tawagar na kunshe da 'yan wasa 16, da kuma sauran jami'ai 9, za kuma ta isa birnin Meizhou dake lardin Guangdong a yau Talata. Daga bisani ana sa ran wasu karin 'yan wasan hudu, da suka hada da mai tsaron baya Faith Michael, da 'yar wasan tsakiya Rita Chikwelu, da 'yan wasan gaba Ini-Abasi Umotong da Chinaza Uchendu za su tarar da su a can.

Sauran kasashe uku da za su buga wannan wasa na kwanaki hudu, sun hada da masaukin baki Sin, da Romania, da Koriya ta kudu. Za kuma a fara taka leda tun daga ranar Alhamis 17 ga watan nan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China