in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadarin mota ya hallaka mutane 14 a jihar Ekitin Najeriya
2019-01-15 09:10:03 cri

Mahukunta sun tabbatar da rasuwar mutane 14, baya ga wasu karin mutanen 5 da suka jikkata, sakamakon tattake mutane da wata babbar mota ta yi, a kasuwar Iworoko dake jihar Ekiti a kudancin Najeriya.

Rahotanni sun ce hadarin ya faru ne a Asabar da ta gabata, lokacin da wata motan dakon kaya ta kwace ta bugi wasu motocin biyu, kafin kuma ta bi ta kan masu saye da sayarwa dake hada hada a cikin kasuwar.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kwamandan shiyya na hukumar kare hadurra ta Najeriya reshen jihar ta Ekiti Kugu Ismaila, ya ce binciken farko ya nuna cewa, motar ta kwacewa direban ta ne, ta kuma shiga cikin kasuwar inda ya yi matukar barna.

Hukumar kare hadurra ta kasar ta bayyana lamarin da hadari mai matukar tayar da hankali, kuma mafi muni da aka fuskanta cikin wannan sabuwar shekaka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China