in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya halarci bikin bude taron ADSW na Abu Dhabi karo na 12
2019-01-14 20:56:41 cri
Yau Litinin a hadaddiyar daular Larabawa, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mamban ofishin siyasa na kwamitin koli na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin Yang Jiechi ya halarci bikin bude taron neman dauwamamman ci gaba na Abu Dhabi wato ADSW a takaice karo na 12 da kuma taron karrama wadanda suka ba da gudummawa a fannin kare muhalli.

A jawabinsa, da farko Yang a madadin shugaba Xi Jinping ya mika sakon taya murnar taron. Inda ya bayyana cewa, shugaba Xi ya nuna cewa, kiyaye muhallin halittu na da muhimmanci sosai ga makomar bil 'Adama, shi ne kuma burin bai daya na jama'ar kasashe daban daban. Ya kamata kasashen duniya su kara hada kai, don tabbatar da samun dauwamamman ci gaba a duk fadin duniya. Sinawa suna da ra'ayin cewa "muhalli mai kyau babban arziki ne", kuma suna kira da a kiyaye kasancewar mutum da muhallinsa, da tsayawa kan hanyar samun ci gaba mai salon kiyaye muhalli da samun dauwamamman ci gaba.

Baya ga haka, Yang da wasu shugabannin da suka halarci taron sun ba da lambobin yabo ga wadanda suka ci nasara a wannan fanni. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China