"Adamawa na fuskantar hali mafi muni a tarihi. Mun damu matuka. Yin garkuwa da neman kudin fansa ya zama ruwan dare a wannan yankin. Kauyuka sun koma kufai kuma tattalin arziki ya sukurkuce," Theophile Baoro, wani wakilin al'ummar yankin Adamawa, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yayin da matsalar ke cigaba da ta'azzara.
An samu rahotannin yin garkuwa da mutane a yankin sama da guda 150 a cikin shekarar da ta gabata, kamar yadda mahukunta yankin suka bayyana. An kiyasta hasarar kudin kasar CFA miliyan 500, kwatankwacin dala dubu 900 wadanda aka biya a matsayin kudin fansa. (Ahmad Fagam)