in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan tattalin arzikin yanar gizo na Sin ya zama matsayin farko a duniya
2019-01-14 11:05:32 cri
A ranar 13 ga wannan wata, sashen nazarin tattalin arzikin yanar gizo da sashen ilmin tattalin arziki na jami'ar ilmin hada-hadar kudi da tattalin arziki ta kasar Sin da kamfanin buga litattafai na kimiyyar zamantakewar al'ummar kasar Sin sun gabatar da rahoton tattalin arzikin yanar gizo na kasar Sin na shekarar 2018, inda aka shaida cewa, yawan tattalin arzikin yanar gizo na kasar Sin ya zama a matsayin farko a duniya.

Rahoton ya bayyana cewa, ma'aunin bunkasuwar tattalin arzikin yanar gizo na kasa da kasa ya shaida kashin yawan tattalin arzikin yanar gizo na kasa da kasa bisa na dukkan manyan kasashen tattalin arzikin duniya. Ma'aunin yana shafar yawan kamfanonin tattalin arzikin yanar gizo, yawan masu amfani da yanar gizo, yawan kayayyakin da aka sayar a kan yanar gizo. Bisa kididdigar da aka yi, an shaida cewa, Sin da Amurka da Japan da Jamus da Birtaniya suna sahun gaba a matsayi na biyar a duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
ga wasu
v An bude taron yanar gizo na duniya karo na 4 2017-12-03 13:08:29
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China