in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya ce ya kamata a koyi fasahar kwaskwarima da bude kofa ta Sin
2019-01-14 11:04:04 cri

Yayin babban taron tayar murnar cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, wanda aka gudanar a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Xi Jinping ya bayyana cewa, sakamakaon da aka samu a cikin shekaru 40 da suka gabata sun shaida cewa, ci gaban kasar Sin ya samar da fasahohi ga kasashe masu tasowa, yayin da suke kokarin samun bunkasuwarsu, ya kuma sa kaimi kan zaman lafiya da ci gaba a fadin duniya.

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa shi ma ya bayyana cewa, kasarsa tana koyon fasahohin kwaskwarima da bude kofa ta kasar Sin, domin ciyar da kanta gaba yadda ya kamata.  

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, wanda yake kokarin raya tattalin arzikin kasa tun bayan da ya lashe zaben shugaban kasa a watan Agustan shekarar 2018, ya kuma bayyana cewa, shi kansa, da sabuwar gwamnatin kasarsa, suna sanya kokari matuka domin aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, ta yadda za su cimma burin raya tattalin arziki, tare kuma da kyautata rayuwar al'ummar kasar. Ya ce yanzu haka sabuwar gwamnatin kasar tana yin nazari kuma tana koyon fasahar samun ci gaban kasa da kasar Sin ta samu a cikin shekaru 40 da suka gabata, yana mai cewa, "Mun lura cewa, kafin shekaru 40 da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wasu matakai domin aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida, da haka ta cimma burin hanzarta saurin zamanantar da tattalin arzikinta, a don haka muna koyon fasahar da kasar Sin ta samu a fannin, ta yadda za mu samu manufar raya kasa da ta dace da yanayin da kasarmu ke ciki."

Shugaba Mnangagwa ya kara da cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin yin gyare-gyare da bude kofa, ya samar da fasahohi da dama ga kasar Zimbabwe, misali a fannin samun daidaito wajen raya birane da kauyuka a kasar, ya ce: "Muna iya koyon fasahohin raya kasa da dama daga kasar Sin, misali mai da hankali kan ci gaban kauyuka, musamman ma wajen samar da wutar lantarki da ruwa mai tsabta, da hanyoyin mota masu inganci, da kasuwa, da sana'o'i daban daban a kauyukan kasar, da haka manoman kauyukan fadin kasar za su shiga aikin yin gyare-gyare da bude kofa a kasar. Kana mun lura cewa, a biranen kasar Sin, kudin shigar Sinawa mazauna birane ya karu cikin sauri. Da yawa daga cikinsu suna fita zuwa kasashen waje domin koyon ilimi da kwarewa ta zamani, daga baya su komo kasar su domin ciyar da kasar Sin gaba."

Shugaba Mnangagwa wanda ya taba yin karatu a kasar Sin a shekarun 1960 ya bayyana cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu a cikin shekarun baya bayan nan ya burge shi kwarai, a bayyane ake iya gano cewa, kasar Sin tana kara zurfafa kwaskwarima a gida da kuma kara bude kofa ga kasashen waje, yana mai cewa, "Ina matukar yabawa tunanin raya kasa na shugaba Xi, kana ina yabawa matakin da ya dauka wajen yaki da cin hanci da rashawa, haka kuma na ga kudin shiga na Sinawa ya karu cikin sauri karkashin kokarinsa, to ina fatan kasarmu ta Zimbabwe, za ta yi amfani da albarkatun kasarmu domin samun ci gaba. Ina ganin cewa, ya kamata mu koyi fasahar da kasar Sin ta samu wajen raya kasa."

Shugaba Mnangagwa ya dauka cewa, dalilin da kasar Sin ta samu babban sakamako a cikin shekaru 40 da suka gabata shi ne, jagoranci mai karfi na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, a don haka jam'iyyar mulkin kasar Zimbabwe dake karkashin jagorancinsa, za ta kara karfafa cudanya dake tsakaninta da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, a cewarsa: "Ko shakka babu za mu kara zurfafa alakar siyasa dake tsakanin kasashenmu, ta hanyar yin musanyar ra'ayoyi kan yadda za su tafiyar da harkokin jam'iyya mai mulkin kasa a sabon zamanin da ake ciki, haka kuma ya dace sassan biyu, su kara yin cudanya tsakaninsu daga duk fannoni, ta yadda za su samu ci gaba tare, ban da haka kuma, za mu kara yin gyare-gyare a gida, haka kuma da fannin tsarin siyasa a kasar."

Hakazalika, shugaba Mnangagwa ya bayyana cewa, yayin da kasarsa take kokarin raya tattalin arzikinta, suna bukatar shigo da sabbin fasahohi da kuma kwarewa, shi ya sa yana fatan kasar Sin za ta kara samar da goyon baya da taimako gare ta.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China