A cewar kamfanin dillancin labarai na Qatar, kudin za su kasance karkashin kulawar kungiyar hadin kan Afirka ta AU, za kuma a kashe su wajen gudanar da dukkanin wasu ayyuka na sufurin 'yan ci ranin daga Libya zuwa kasashen su.
Hakan dai na zuwa ne a gabar da shugaban hukumar zartaswar kungiyar ta AU Moussa Faki ke ziyarar aiki a birnin Doha na Qatar a jiya Lahadi. Yayin ziyarar ta sa, sassan biyu sun tattauna game muhimman batutuwa dake jan hankulan su. (Saminu Hassan)