in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Motoci masu amfani da sabbin makamashi na bunkasa cikin sauri a kasar Sin
2019-01-13 16:55:25 cri
Ministan kula da harkokin masana'antu da sadarwa na kasar Sin Miao Wei, ya bayyana a jiya Asabar cewa, a shekarar da ta gabata, duk da cewa sana'ar kera motoci ta kasar bata bunkasa sosai ba sakamakon dalilai da dama, amma zata samu bunkasuwa a nan gaba, musamman sana'ar kera motoci masu amfani da sabbin makamashi.

A wajen taron dandalin tattaunawa kan motoci masu amfani da karfin wutar lantarki da aka yi jiya Asabar, Miao Wei ya bayyana cewa, sana'ar kera motoci masu amfani da sabbin makamashi ta kara habaka. A shekarar 2018 data gabata, adadin yawan motoci masu amfani da sabbin makamashi da aka kera a kasar Sin ya kai miliyan 1.27, kana, yawan motocin da aka sayar da su ya kai kusan miliyan 1.26, wadanda suka karu da kashi 59. 9 bisa dari da kashi kuma 61.7 bisa dari.

Har wa yau, Miao ya ce, a nan gaba kasar Sin zata ci gaba da tsayawa kan yin gyare-gyare ga bangaren samar da kayayyaki, da aiwatar da manufofi daga fannoni daban-daban, a wani kokari na raya sana'ar kera motoci masu amfani da sabbin makamashi yadda ya kamata.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China