in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi hadari a wani wurin hakar ma'adinin kwal a birnin Shenmu na lardin Shaanxi na kasar Sin
2019-01-13 16:52:38 cri
Rahotanni daga gwamnatin birnin Shenmu na lardin Shaanxi dake yammacin kasar Sin sun ruwaito cewa, wani hadarin da ya wakana a jiya Asabar a wani wurin hakar ma'adinin kwal dake birnin ya sa mutane 21 sun makale, ciki har da mutane 19 wadanda suka rasa rayukansu, yayin sauran biyu kuma ake kokarin ceto su.

Bayan aukuwar hadarin, gwamnatin birnin Shenmu ta fara daukar matakan daukin gaggawa, inda aka tura ma'aikatan ceto wurin don gudanar da aikin ceto da tallafawa mutanen da abun ya shafa.

A waje guda kuma, ma'aikatar kai daukin gaggawa ta kasar Sin ta tura wata tawaga zuwa wurin, don bayar da jagoranci ga ayyukan ceto da gudanar da bincike kan aukuwar hadarin. A halin yanzu ana nuna himma da kwazo wajen gudanar da ayyukan ba da tallafi da ceto da binciken musabbabin aukuwar hadarin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China