A yayin ganawar tasu, Yang Jiechi ya bayyana cewa, a shekarar 2018 da ta wuce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Saliyo Madda Bio, a yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wanda aka yi a birnin Beijing, inda shugabannin biyu suka cimma matsaya kan wasu manyan batutuwa. Kasar Sin tana son zurfafa zumuncin gargajiya dake tsakaninta da kasar Saliyo, karfafa fahimtar juna dake tsakaninsu a fannin siyasa, habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa dukkan fannoni, karfafa mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu kan harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, domin kiyaye moriyar kasashen biyu, har ma da dukkanin kasashe masu tasowa.
A nasa bangare kuma, Mr. Kabba ya ce, shugaban kasarsa Madda Bio, ya cimma nasarar ziyarar aiki a kasar Sin a shekarar 2018. Kasar Sin ita ce aminiyar kasar Saliyo, shi ya sa, kasar Saliyo tana fatan yin hadin gwiwa da kasar Sin domin ci gaba da inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Maryam)