in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na fatan tallafawa nahiyar Afirka wajen bunkasa cinikayya ta amfani da fasahar sadarwa
2019-01-11 20:29:39 cri
Daraktan hukuma mai lura da aikewa da sakwanni ta MDD ko UPU a takaice Bishar Hussein, ya ce hukumar sa na shirin fidda wani tsari, na tallafawa nahiyar Afirka da dabarun cin gajiyar cinikayya ta yanar gizo, ta yadda nahiyar za ta samu karin bunkasar tattalin arziki a wannan fanni.

Bishar Hussein, ya bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a yau Juma'a a birnin Nairobin kasar Kenya. Ya ce tsarin amfani da yanar gizo wajen gudanar da cinikayya, zai gudana ne bisa dandalin Ecom@Africa, inda za a baje kolin hajojin da ake samarwa a daukacin sassan nahiyar ga masu sayayya na dukkanin bangarorin duniya. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China