Shugaban ya ce akwai bukatar fadada kwazo, wajen inganta ayyukan jam'iyya, da kuma tabbatar da cimma manyan kudurori, da gudanar da ayyukan gwamnati bisa doka.
Xi, wanda kuma shi ne shugaban hukumar zartaswa ta rundunar sojojin kasar Sin, ya ja hankalin masu ruwa da tsaki, wajen ci gaba da aikin tabbatar da wanzuwar nasarorin da aka riga aka samu a fannin yaki da cin hanci. (Saminu Hassan)