Yayin ganawar, babban jami'in kasar Sin ya ce, ya kamata kasashen 2 su yi kokarin yaukaka dankon zumuncin dake tsakaninsu, da kara musayar ra'ayoyinsu game da harkokin da suka shafi kasashen 2, da sauran sassan duniya baki daya. Za a kuma kara kokarin aiwatar da manufofin da aka gabatar wajen taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana bara.
A nashi bangaren, ministan wajen kasar Saliyo, ya ce kasarsa na son koyon dabarun raya kasa na kasar Sin, da zurfafa hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen 2, da kara kyautata huldar dake tsakaninsu.
A nasa bangare, mamban majalisar gudanarwa kuma ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, shi ma ya gana da mista Alie Kabba.(Bello Wang)