in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanzu al'ummomin Sinawa na kokarin kare 'yancin mallakar fasaha
2019-01-11 19:01:20 cri

A kwanakin baya, direktocin hukumomin kare 'yancin mallakar fasaha na matakai daban daban na sassan duk kasar Sin sun taru a nan Beijing fadar mulkin kasar, inda suka takaita ayyukan kare 'yancin mallakar fasaha da aka yi a shekarar 2018 da kuma tsara shirin kare 'yancin mallakar fasaha na shekarar 2019, ta yadda za a iya sa kaimi kan kirkiro sabbin fasahohin zamanin da kuma bunkasa tattalin arziki mai inganci.

Bisa kokarin da aka yi cikin shekaru 40 da suka gabata bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga waje, musamman bayan da aka kaddamar da "manufar kare 'yancin mallakar fasaha ta kasar" a shekarar ta 2008, an sa kaimi da kuma gyara "dokar kare ikon mallakar kira" da "dokar kare tambarin kaya" da "dokar kare ikon wallafe-wallafe" da makamatansu, sannan an kafa kotun kare 'yancin mallakar fasaha domin tabbatar da ganin an inganta karfin kare 'yancin mallakar fasaha. Sau da dama ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada muhimmancin kare 'yancin mallakar fasaha a yayin taruka da dama, inda ya nuna cewa, shi ne aiki mafi muhimmanci ga kokarin inganta dokokin kare mallakar fasaha, har ma shi ne zai fi sa kaimi ga inganta karfin gogayyar tattalin arzikin kasar Sin a kasuwa.

Cikin taro na wannan karo, an takaita ayyukan shekarar 2018, inda aka bada misalai da dama, ciki har da kammala ayyukan yin kwaskwarima a hukumomin kula da 'yancin mallakar fasaha na kasa da na lardunan kasar Sin, da daidaita ayyukan kula da tambarin kaya da lambar kira da dai sauransu. Bisa kididdigar da aka yi, ban da a yankunan Hong Kong, Macao da Taiwan, ya zuwa karshen shekarar 2018, adadin kayayyaki masu lambar kira da aka samar ya kai sama da miliyan 1.6 a kasar Sin, wanda ya karu da kashi 18.1%. Kuma adadin tambarin cinikin da aka yi rajista a kasar Sin ya kai sama da miliyan 18, adadin da ya karu da kashi 32.8%. Bugu da kari, adadin kayayyaki na alamar kasa da aka ba su izini ya kai guda 2380, kana, adadin tambarin ciniki na alamar kasa ya kai guda 4867.

Hukumar tsara dokoki ta kasar Sin ta kammala aikin tantance gyaran daftarin dokar kare hakkin mallakar kira, sa'an nan an shigo da tsarin biyan diyya a matsayin wani hukuncin da aka yankewa masu laifi. Ban da haka kuma, yawan kudin da aka biya wajen yin amfani da hakkin mallakar kira a kasar ya zarce dalar Amurka biliyan 35...

Wadannan lamura da alkaluma sun shaida cewa: kasar Sin ta riga ta zama wata babbar kasa a fannin kare 'yancin mallakar fasaha. Yanzu a kasar ana kara samun karfin kirkiro sabbin fasahohi, kana masana'antu masu alaka da sabbin fasahohi su ma suna samun ci gaba. Alal misali, tsarin Beidou na yin amfani da taurarin dan Adam wajen bada jagoranci ga aikin zirga-zirga, wanda aka fara yin amfani da shi wajen samar da hidima ga kasashe daban daban. Wannan tsarin kasar Sin tana da cikakken 'yanci na mallakar fasahohin da ya kunsa. Sa'an nan yayin da ake kokarin samar da tsarin, masana kimiyya da fasaha na kasar Sin sun daidaita daruruwan matsaloli, tare da gabatar da sabbin fasahohi, ta yadda aka samu karuwar fasahohi a wannan fanni matuka. Tun bayan shekarar 2012, yawan bukatun da aka gabatar don neman samun hakkin mallakar kira mai alaka da tsarin Beidou ya zarce dubu 11. Ban da haka, wani kawancen da aka kafa don kare hakkin mallakar kira mai alaka da tsarin Beidou, shi ma ya taimakawa aikin kirkiro sabbin fasahohi a wannan fanni.

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, jimillar GDP da kasar Sin ta samu ta sana'ar dake bukatar ikon mallakar ilmin kirkire-kirkire ya kai kashi 12.4 cikin dari a halin yanzu.

"Kiyaye 'yancin mallakar fasaha shi ne kiyaye kirkire-kirkire", "kyautata kwarewar kirkire-kirkire za ta taimaka wajen kare 'yancin mallakar fasaha"… irin wannan ra'ayi ya riga ya samu amincewa daga jama'ar Sin sosai, yanzu kamfanoni masu jarin waje da yawa sun fi son zuwa kasar Sin don gabatar da kararrakinsu ta fuskar neman 'yancin mallakar fasaha, yayin da kamfanonin Sin masu dimbin yawa na yin amfani da fasaharsu ta kiyaye 'yancin mallakar fasaha wajen fadada kasuwannin duniya. Kamfanonin kasa da kasa sun bullo da sabbin fasahohi da sabbin kayayyaki fiye da 100 a yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin da aka yi a watan Nuwamban bara. Dalilin da ya sa suka yi hakan shi ne saboda ba ma kawai sun maida hankali kan kasuwar kasar Sin ba, hatta ma da yadda kasar Sin ke yin kokari don kare 'yancin mallakar fasaha da ma kyawawan sakamakon da ta samu a wannan fannin.

A hakika, kasar Sin tana kokarin kare 'yancin mallakar fasaha. Alal misali, tattara shaidu ba abu ne mai sauki ba kuma ana kashe kudi mai yawa amma samun kudin diyya kadan a bangaren kare 'yancin mallakar fasaha. Haka kuma duk da cewa adadin yawan mutanen da suka nemi samun 'yancin mallakar fasaha a kasar Sin ya zama na farko a duk fadin duniya a cikin jerin shekaru bakwai, amma ba su da karfi sosai idan aka kwatanta da na sauran kasashe. Har wa yau, kasar Sin na nuna himma da kwazo wajen kara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a halin yanzu, al'amarin dake bukatar a rubanya kokarin kare 'yancin mallakar fasaha.

Bana shekara ce ta farko tun bayan da kasar Sin ta kammala aikin yin kwaskwarima ga hukumomin kare 'yancin mallakar fasaha. A wajen taron shugabannin hukumomin kare 'yancin mallakar fasaha da aka yi a wannan karo, an bayyana muhimman ayyukan da za'a gudanar a bana daga wasu fannoni tara, ciki har da kara duba 'yancin mallakar fasaha, da kara kare 'yancin mallakar fasaha, da yin amfani da 'yancin mallakar fasaha a bangarori da dama, da karfafa sa ido kan bangaren 'yancin mallakar fasaha daga dukkan fannoni, tare kuma da zurfafa hadin-gwiwar kasa da kasa wajen kare 'yancin mallakar fasaha da sauransu.

Daga cikinsu, shirye-shiryen da suka hada da gyaran dokar kare tambarin kaya da inganta dokokin da suka shafi kare 'yancin mallakar fasaha da nazarin 'yancin mallakar fasaha sun shaida yadda kasar Sin ke kare 'yancin mallakar fasaha bisa hakikanin yanayin da take ciki tare da daidaita sabbin kalubale da matsalolin da take fuskanta, da kuma yadda take bude kofarta wajen hadin gwiwa da kasa da kasa ta fannin kare 'yancin mallakar fasaha.

A yayin da karin kamfanonin kasar Sin ke gudanar da harkokinsu a ketare, kasar Sin ma tana fatan gwamnatin kasashen za su kara karfin kare 'yancin mallakar fasahohi na kamfanonin. Alkaluman da kasar Amurka ta fitar a kwanan baya sun shaida cewa, a shekarar 2018, kamfanonin kasar Sin sun samu lambobin kira sama da dubu 12.5, adadin da ya karu da kaso 12% bisa na shekarar ta 2017, wanda har ya kai wani matsayin koli a tarihi.

Yawan lambobin kira da hukumar bada lambar kira da tambarin ciniki ta kasar Amurka ta bayar a shekarar bara ya ragu da kashi 3.5 cikin dari bisa na shekarar 2017, sai dai kamfanonin kasar Sin yawan lambobin kira da suka samu ya karu bisa na bara. Wannan ya nuna cewa, kwarewar kasar Sin na yin kirkire-kirkire na karuwa, kuma kasashen duniya na kara karfin kiyaye 'yancin mallakar fasaha na kasar Sin.

Akwai wanda ya kwatanta cewa, 'yancin mallakar fasaha ya zama tamkar wata gada, wadda ke hada ayyukan yin kirkire-kirkire da kasuwanni. Bisa karuwar karfin kasar Sin na daukar matakai a fannin kare 'yancin mallakar fasaha, za a inganta ayyukan yin kirkire-kirkire, ta hakan za a sa kaimi kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin mai inganci da ma ci gaban duniya baki daya. (Sanusi Chen, Bello Wang, Maryma Yang, Kande Gao, Murtala Zhang, Bilkisu Xin, Lubabatu Lei)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China