"Daukar matakan soji, duk da cewa sun zama tilas, amma hakan ba zai wadatar ba" inji Mohamed Ibn Chambas, wakilin musamman na babban sakataren MDD a yammacin Afrika da yankin Sahel, ya jaddada bukatar daukar matakan da suka dace.
A yankin tafkin Chadi, akwai karuwar hare haren mayakan Boko Haram a watannin baya bayan nan, mayakan na kokarin yaki da dakarun sojojin da aka girke a yankunan, in ji shi, ya kara da cewa, ana cigaba da samun rikicin manoma da makiyaya, amma ya ragu.
A Nijer, duk da tura dakarun tsaro da na wanzar da zaman lafiya, har yanzu, suna cigaba da fuskantar kalubaloli a yankunan yamma da kudancin kasar," in ji wakilin MDD.
Duk da karuwar matsalar kalubalolin tsaro, Chambas ya yaba da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa a Mali a bara, da zabukan wakilan shiyyoyi a kasar Mauritania, da kuma zabuka a kasashen Togo da Cote d'Ivoire, ya kara da cewa, duk da irin cigaban da aka samu wajen tabbatar da tsarin demokaradiyya a shiyyar, akwai bukatar cigaba da kokari wajen shawo kan kalubalolin da suka shafi harkokin zabuka a shiyyoyin."
Wakilin MDDr yace, akwai bukatar daukar matakan da suka dace, kasancewar a cikin watanni 6 masu zuwa shiyyar zata tunkari manyan zabuka masu yawa da suka da kasashen Najeriya, Senegal, Mauritania da jamhuriyar Benin.