in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana goyon bayan manufofin WTO kan tsarin cinikayyar shiyya cikin 'yanci
2019-01-11 10:40:06 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar cinikayyar kasar Sin Gao Feng, ya bayyana cewa, kasarsa tana goyon bayan bullo da yarjejeniyar cinikayyar shiyya cikin 'yanci kamar yadda manufofin kungiyar cinikayya ta duniya suka tanada.

Da yake yiwa taron maname labarai karin haske kan yarjejeniyar hadin gwiwar kasashe 11 dake yankin tekun fasifik,Gao Feng ya ce a halin yanzu, kasashen da abin ya shafa suna son ganin gudanar yarjeniyoyin cinikayayyar shiyya cikin 'yanci, inda suke fatan ganin an samu bunkasar harkokin cinikayya da zuba jari cikin 'yanci. Duba da yadda tattalin arzikin duniya ke ci gaba da dunkulewa waje guda. Ya ce matsayin kasar Sin kan irin wannan tsari bai canja ba.

Gao ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan tsarin cinikayya tsakanin kasashe daban-daban, da bullo da matakan cinikayyar shiyya cikin 'yanci bisa manufofin WTO mai salon bude kofa da samun moriya tare ba tare da wata rufa-rufa ba.

Yanzu haka kasar Sin da sauran bangarori na kokarin ganin an sasanta da sassan da abin ya shafa game da hadin gwiwar shiyya-shiyya kan harkokin tattalin arziki (RCEP), wani yankin cinikayya cikin 'yanci da ake fatan kafawa tsakanin sassa 16 da ya kunshi kusan rabin al'ummar duniya, tsarin da ya kunshi sama da kaso 31 cikin 100 na GDPn duniya baki daya.

A karshen shekarar da ta gabata ce dai, yarjejeniya da ta kunshi sassa ko kasashe 11 ta fara aiki a hukunce.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China