in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya sanar da soke zuwa Davos
2019-01-11 10:35:10 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da soke ziyarar da ya shirya kaiwa Davos na kasar Swiss don halartar taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arziki na kasa da kasa.

Trump ya sanar da yanke shawara ce a jiya Alhamis a dandalin sada zumunta, inda ya ce, ya soke ziyarar ce sakamakon matakin da 'yan jam'iyyar democrats a majalisar dokokin kasar suka dauka game da batun tsaron kan iyaka, da kuma muhimmancin tsaro ga kasar Amurka.

Sakamakon bambancin ra'ayi tsakanin fadar White House da 'yan jam'iyyar ta democrats game da gina katanga a iyakar kasar da wasu sauran batutuwa, ya sa bangarori daban daban gaza cimma matsaya kan shirin dokar da za ta samar da kudaden da shugaban ke bukata. Kimanin kaso 1 cikin 4 na hukumomin gwamnatin tarayyar Amurka ne aka rufe tun daga safiyar ranar 22 ga watan Disamban shekarar da ta gabata. Fadar White House da 'yan jam'iyyar democrats dai sun sha yin shawarwari, tun lokacin da aka rufe ma'aikatan tarayyar kasar, amma babu wani takamammen ci gaba da aka samu.

Za a gudanar da taron shekara-shekara na bana na dandalin tattaunawar tattalin arzikin kasa da kasa a tsakanin ranar 22 zuwa 25 ga wata a Davos na kasar Swiss. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China