Jami'in ya ce tawagar MDD dake kasar, na ci gaba da bibiyar abubuwan dake faruwa a kasar, ko da yake tawagar ta ce, al'amura na gudana yadda ya kamata a kasar.
Bayan sanar da sakamakon zaben shugabancin kasar na ranar 30 ga watan Disamban shekarar da ta gabata, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, da su guji tayar da zaune tsaye, kana su gabatar da duk wani kokensu na zabe ta hanyoyin da doka ta tanada.
Babban sakataren MDDr ya kara nanata kuduri da goyon bayan majalisar na ci gaba da hada kai da masu ruwa da tsaki na shiyya da abokan huldar kasa da kasa, na ganin an samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma ci gaba a kasar.(Ibrahim)