in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An yi murnar aza harsashin gina ma'aikatar kamfanin Tesla a kasar Sin
2019-01-10 19:41:07 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya furta a yau Alhamis cewa, ya yi murnar aza harsashin ginin kamfanin Tesla mai samar da motocin dake aiki da lantarki na kasar Amurka a kasar Sin. Kamfanin Tesla ya fara gina reshen ma'aikatarsa na farko dake wajen kasar Amurka a birnin Shanghai na kasar Sin.

A cewar jami'in, kasar Sin tana tsayawa kan manufarta ta bude kofa, da huldar hadin gwiwa irinta amfanar juna, sa'an nan kasar na maraba da karin kamfanonin ketare, da su yi amfani da damammakin da ci gaban kasar Sin ke samarwa. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China