Jami'in ya kara da cewa, a ranar 15 ga watan da muke ciki, babban bankin kasar Sin, zai rage yawan kason kudin ajiya da hukumomin kudi su kan ajiye a bankin tsakiya da kashi 1%, ta wannan hanyar kuma za a samar da kudin da yawansu ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 1500, wadanda za a iya amfani da su.
Ban da haka, a karshen watan Janairun bana, za a dauki matakin saukaka ayyukan samar da rance na matsakaicin wa'adi. A cewar jami'in, duk wadannan matakai za su taimaka, wajen shigar da isassun kudi cikin kasuwa, da tabbatar da wani yanayi na karko ga yawan ruwan kudin da ake karba a kan bashi, gami da sanya rancen da ake samu ya karu daidai wa daida. (Bello Wang)