in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta samar da matakai don raya yankin da gwamnati ta cire masa haraji
2019-01-10 19:39:39 cri
Kasar Sin tana shirin gabatar da wasu matakai, don karfafa ayyukan bude kofa a kebabbun wuraren masana'antu da gwamnati ta cire musu haraji. Dangane da hakan, mataimakin darektan babbar hukumar kwastam ta kasar Sin Li Guo, ya sanar a yau Alhamis a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin cewa, za a gabatar da wasu sabbin manufofi 21, don taimakawa raya yankunan da gwamnati ta cire musu haraji, wadanda suka hada da rage harajin da kamfanoni suke biya, da tallafawa 'yan kasuwan dake shigo da kayayyaki daga ketare, wadanda za su sayar da su ta kafar yanar gizo ta Intanet, da dai sauransu. Burin hakan shi ne baiwa kebabbun yankunan damar samun ci gaba a fannoni daban daban. (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China