A cewar Wang, don kara kyautata huldar da ke tsakanin Sin da Amurka, kamata ya yi kasashen 2 su tsaya kan manufar samar da dadaito, da hadin kai, da yanayi na kwanciyar hankali don amfanin jama'ar bangarorin 2, gami da ta daukacin duniya baki daya.
Jami'in ya kara da cewa, ra'ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma, ya nuna alkiblar da za a nufa, yayin da ake kokarin raya huldar dake tsakanin bangarorin 2. Ya ce wannan huldar ta riga ta zama irinta mafi tasiri a duniya, wadda kuma za a iya kara kyautata ta a nan gaba.
Ban da haka, cikin wadannan shekaru 40, kasashen Sin da Amurka sun haye wahalhalu, suna kuma ta kokarin raya huldar dake tsakaninsu, tare da cimma nasarori sosai. Wadannan nasarori, a cewar jami'in, sun haifar da babbar moriya ga jama'ar bangarorin 2, gami da taimakawa wanzuwar zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da kuma zaman walwala a duniyarmu. (Bello Wang)