in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tshisekedi ya lashe zaben jamhuriyar dimokuradiyyar Congo
2019-01-10 19:32:17 cri
Hukumar zaben kasar jamhuriyar dimokuradiyyar Congo, ta bayyana dan takarar jam'iyyar adawa Felix Tshisekedi, a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar, bisa alkaluman wucin gadi da hukumar ta fitar da sanyin safiyar Alhamis.

A cewar hukumar Tshisekedi na jam'iyyar UDPS, ya samu yawan kuri'u sama da miliyan 7 daga sassan kasar daban daban, in ban da birane uku da ba a kammala zabe a cikin su ba sakamakon tashe tashen hankula.

Mr. Tshisekedi ya shige gaban dan takarar jam'iyya mai mulkin kasar Martin Fayulu, da kuma dan takarar jam'iyyun hadaka na masu mulkin kasar Emmanuel Ramazani Shadary. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China