in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya Kamata Sin Da Amurka Su Kara Kokari Tare Don Samun Sakamako Nafi Gamsarwa
2019-01-10 17:27:28 cri


An kammala shawarwari kan batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin mataimakan ministocin Sin da Amurka jiya Laraba a birnin Beijing, shawarwarin ne da suka kasance irinsu na farko da bangarorin biyu suka gana da juna fuska da fuska, don aiwatar da muhimman ra'ayoyi iri daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a kasar Argentina, inda bangarorin biyu suka zurfafa musayar ra'ayoyi da tattaunawa kan harkokin cinikayya da tsare-tsare da sauran batutuwan da suka jawo hankalinsu duka. Duk da cewa an dage shawarwarin da rana daya, amma bangarorin biyu sun kara samun fahimtar juna, al'amarin da ya aza tubali mai inganci ga daidaita matsalolinsu.

Bisa sakamakon da aka samu a gun shawarwarin, bangarorin biyu sun cimma ra'ayin bai daya kan batun cinikayya, ciki har da batun kasar Sin za ta kara habaka shigo da kayayyakin aikin gona da na makamashi daga kasar Amurka, hakan za a kara biyan bukatun masu sayayya na kasar Sin kan zaman rayuwa mai inganci, da ciyar da tattalin arzikin kasar gaba yadda ya kamata. Ko shakka babu, kasar Sin na habaka shigo da kayayyaki ne daga duk duniya. An ce, a yayin shawarwarin, kasar Amurka ta gabatar da hakikanin bukatunta, ciki har da bukatar kasar Sin ta tabbatar da hakikanin lokacin shigo da kayayyaki daga kasar Amurka da dai sauransu. A zahiri, kason kayayyakin kasar Amurka bisa kasuwar kasar Sin na dogaro da bukatun masu sayayya na kasar Sin ne.

Yayin tattaunawar dake tsakanin sassan biyu, wakilan kasar Amurka sun gabatar da wasu batutuwa game da tsarin tattalin arziki, wadanda ke shafar tsarin kasar Sin ko tsaron kasar ko manufofin kasar, ba zai yiwu ba gwamnatin kasar Sin ta amince da su, kana wasu suna shafar manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, haka kuma ana kokarin daidaita su ko kusan warware su cikin nasara a nan kasar Sin, misali batu game da kare ikon mallakar fasaha, yanzu a kasar Sin ana sanya kokari matuka domin raya kasa ta hanyar yin kirkire-kirkire, don haka tabbas ne kasar Sin za ta kara daukan matakai domin tabbatar da aikin, kwanan baya majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato hukumar tsara dokokin kasar ta bincike daftarin dokar ikon mallakar fasaha, inda a karo na farko ne aka rubuta cewa, za a biya kudin diyya domin hukunta wadanda suka take ikon mallakar fasaha.

Yanzu kasar Sin ta shiga wani muhimmin mataki wajen gudanar da gyare-gyare, kuma kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kwatanta yanayin da ake ciki da cewa, "jirgin ruwa ya kan fi fuskantar barazanar ambaliya idan ya kai tsakiyar kogi, kuma mutum zai fi fuskantar wahala idan ya kai tsakiyar zango a lokacin hawan dutsen, wato an shiga wani yanayi na kara fuskantar wahala, kuma idan ba a yi kokarin samun ci gaba ba, lalle za a yi koma baya." Don haka, ko akwai takaddamar ciniki a tsakanin Sin da Amurka ko babu, kuma batutuwa kamar su kare hakkin mallakar fasaha da hadin gwiwar fasaha da izinin shiga kasuwa da shingayen ciniki da ba na kudin kwastam ba, dukkansu batutuwa ne da dole ne kasar Sin ta daidaita a lokacin da take neman ci gaba mai inganci. Yadda kasashen Sin da Amurka suka cimma daidaito kan wadannan batutuwa, ya biya bukatun da ake da su na kara inganta gyare-gyare da bude kofa a kasar Sin.

Bayan watanni 9 da tsanantar rigingimun tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, bangarorin biyu sun samu ci gaba a shawarwarin da suke tsakanin mataimakan ministocinsu. Wani muhimmin dalilin da ya sa haka shi ne, saboda dukkannin bangarorin biyu da ma duk duniya sun dandana kudar rigingimun.

Tun bayan tsakiyar watan Oktoban bara, ana ta samun tangardar kasuwar takardun hada-hadar kudi a Amurka, gibin kudi wajen cinikayya a tsakanin Sin da Amurka ya kai dala biliyan 50.5 a watan Nuwamban bara, wanda ya zama mafi tsanani a cikin wadannan shekaru shida da suka wuce. Ban da wannan kuma, jimillar PMI na masana'antu ya ragu sosai har ma ya kai mafi kasa a cikin shekaru biyu da suka shude. A waje daya kuma, jimillar PMI na kasar Sin a watan jiya ya ragu har kasa da ma'aunin imanin da 'yan kasuwa ke nunawa tattalin arzikin.

Game da yanayin kamfanonin kasar Amurka, a sakamakon fuskantar rikicin ciniki dake tsakanin Sin da Amurka, kamfanin GM na kasar Amurka ya sanar da rufe kamfanoninsa na duniya guda 7 a karshen watan Nuwamba, darajar kasuwar kamfanin Apple ta rage dala fiye da biliyan 400 a watanni 3 da suka gabata, don hakan kamfanin Apple ya rage tsammanin kudin shigarsa na watanni 3 na karshe na bara. Yawan kamfanonin kasar Amurka da suka halarci bikin baje koli na kayayyakin da ake shigar da su kasar Sin a karo na farko ya kai kimanin 180, yawansu ya kai kashi daya cikin uku bisa na kasar Japan, amma yawan kamfanonin kasar Sin da suka halarci bikin baje koli na fasahohin sadarwa na kasa da kasa da aka gudanar a birnin Las Vegas ya rage kashi 20 cikin dari bisa na shekarun baya.

A shekarar 2018, mai iyuwa ne, saurin karuwar cinikin kayayyakin dake tsakanin kasa da kasa ya ragu da 0.3%. Kwanan baya, bankin duniya ya rage hasashen karuwar tattalin arziki na shekarar 2019 da shekarar 2020 zuwa 2.9% da 2.8%, adadin da ya ragu da 0.1% idan aka kwatanta da hasashen da ya yi a watan Yuni na shekarar 2018. Bisa labarin da jaridar New York Times ta fidda, an ce, takkadamar ciniki ta bata yanayin kasuwannin hada hadar kudi da yanayin tattalin arzikin duniya, shi ya sa, kullawar yarjejeniyar ciniki dake tsakanin Sin da Amurka ba kawai ta dace da fatan Sin da na Amurka ba ne, har ma ta kasance fatan kasa da kasa.

Bisa ra'ayi daya da shugabannin Sin da Amurka suka cimma a wajen ganawarsu, an kebe kwanaki 90 domin a yi mu'amala tsakanin bangarorin 2. Zuwa yanzu, kwanaki 50 ne suka rage ke nan. Saboda haka, ana fuskantar wani yanayi na kurewar lokaci, yayin da ake jiran samun wata yarjejeniya tsakanin kasashen 2. A wannan karo, an samu ci gaba wajen shawarwarin da aka yi tsakanin manyan jami'an kasashen 2, kana sun yarda da ci gaba da kokarin musayar ra'ayi tsakaninsu, wannan wani mafari ne mai kyau.

Takaddamar tattalin arziki da ciniki da ake samu tsakanin Sin da Amurka tana da sarkakiya sosai. Saboda haka, ko da yake, kasar Sin, bisa matsayinta na wadda ta mayar da martani ga matakan da Amurka ta fara dauka, ta yi iyakacin kokarinta don ganin an kawar da sabanin dake tsakanin bangarorin 2, tare da nuna cikakken sahihanci, amma duk da haka, ana bukatar kokari na dukkan bangarorin Sin da Amurka kafin su samu kulla wata yarjejeniya tsakaninsu.

A cikin watanni 9 da wani abu, juriyar tattalin arziki da babbar kasuwa da kasar Sin take da su sun samu horo a lokacin da ake yin takkadamar cinikayya tsakanin kasar Sin da kasar Amurka. Kamfanin Tesla na kasar Amurka ya bude masana'antarsa mai girma sosai ta farko a birnin Shanghai na kasar Sin ya shaida cewa, kasuwar kasar Sin tana da karfin jawo hankulan baki 'yan kasuwa sosai. Tsayawa tsayin daka kan matsayin tafiyar da harkokinta da kanta, da kara yin gyare-gyare da bude kofarta ga waje bisa sabbin ma'aunai, yanzu sun kasance ba kamar wasu kalmomi kawai ba, sun kasance matakan gani ne da kasar Sin take dauka kamar yadda ake fata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China