in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin kan Sin da kasashen duniya wajen binciken sararin samaniya
2019-01-10 14:54:26 cri


Sinawa na ganin cewa, sararin samaniya mallakar dukkanin 'yan Adam ne, don haka, a shekarar 2018 da ta shude, kasar Sin ta samar da albarkatun da take da su, kuma ta hada kanta da kasashen duniya wajen binciken sararin samaniya.

A yayin da kasar Sin ke hada kanta da kasashen duniya, ta samar da albarkatun da take da su. A ranar 8 ga watan Disamban shekarar 2018, kasar Sin ta harba na'urar binciken duniyar wata ta Chang'e-4, wadda a ranar 3 ga wannan wata ta sauka a bayan duniyar wata, sa'an nan, ta aiko wani hoton bayan duniyar wata zuwa gida ta tauraron dan adam na "Queqiao". Kana, wannan shi ne hoton bayan duniyar wata na farko da wata na'urar da bil Adama ya kera ta dauka. A cikin shekaru 60 da suka wuce, na'urorin binciken wata da 'yan Adam suka harba sun wuce 100, sai dai babu wadda ta sauka a bayan duniyar wata. Mr. Wu Weiren, babban mai kula da aikin binciken duniyar wata ta kasar Sin ya ce, na'urar bincike ta Chang'e-4 da aka harba za ta taimaka ga samun karin fahimtar wannan bangaren da ba a san kome ba. Ya ce, "Ko kadan dan Adam bai taba zuwa bayan duniyar wata ba, amma ga shi yanzu mun sauka a wurin, inda kuma muka gudanar da bincike. Akwai yanayi da kuma sinadarai da dan Adam bai sani ba a game da bayan duniyar wata, don haka dole ne mu je mu gudanar da bincike, wanda zai taimaka ga ci gaban dan Adam baki daya."
A yayin da na'urar bincike ta Chang'e-4 ke gudanar da bincike, tana kuma daukar na'urorin bincike na wasu kasashe hudu, a game da wannan, Mr. Zhang Kejian, shugaban hukumar kula da masana'antu da kimiyyar tsaron kasa ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Har kullum gwamnatin kasar Sin na tsayawa kan hada kan kasa da kasa wajen binciken sararin samaniya bisa tushen zaman daidaito da samun moriyar juna da zaman lafiya da kuma yin hakuri da juna. A yayin da muke gudanar da binciken duniyar wata, mun yi kokarin samar da albarkatun da muke da su, kuma muka dauki na'urorin bincike na kasashen Saudiyya da Sweden da Jamus da kuma Holland bisa na'urar bincike ta Chang'e-4 da kuma tauraron dan Adam na Queqiao, don mu saukar da na'urar bincike a bayan duniyar wata a karo na farko, tare da bada taimakonmu a fannin binciken sararin samaniya."

Baya ga haka, taurarin dan Adam da kasar Sin ta harba suna samar da bayanai da hidimomi a duniya baki daya. Tsarin taurarin dan Adam na Beidou dake samar da jagorancin zirga-zirga tsari ne da kasar Sin ta samar, kuma ya zuwa watan Nuwamban bara, an kammala wani kashi da ake kira Beidou-3, wanda kuma ya fara aiki a karshen shekarar bara, kuma yana samar da hidimar bada jagorancin zirga-zirga ga kasashe da yankunan da shawarar nan ta ziri daya da hanya daya ta shafa.

Baya ga wannan, taurarin dan Adam na Fengyun da kasar Sin ta harba suna kuma samar da bayanai ga kasashe da shiyyoyi sama da 80 a duniya. kasar Sin ta harba tauraron dan Adam samfurin Fengyun-2H a watan Yunin bara, kuma bayan da aka kammala gwajinsa a kan hanyar da yake bi, an daidaita hanyarsa, ta yadda zai iya kara hade yankin kasar Sin da kasashen da shawarar ziri daya da hanya daya ta shafa da kuma kasashen dake yankin tekun Indiya da daukacin kasashen Afirka, a game da wannan, Mr. Zhao Jian, mataimakin shugaban sashen harkokin injiniya na hukumar kula da kimiyya da masana'antu na tsaron kasa ta kasar Sin ya ce, "Hukumar kula da yanayin duniya ta gabatar da wannan bukata gare mu, kuma kasashe da dama sun amsa sosai bayan da kasar Sin ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya. A cikin irin wannan hali ne, bayan da masana suka tattauna suka kuma gwada, sai muka daidaita hanyar da tauraron ke bi zuwa yamma, ta yadda zai iya shafar daukacin kasashen Turai da ma kasashen Afirka da na gabas ta tsakiya, matakin da ya taimaka ga kyautata kwarewarmu wajen yin hasashen yanayi a kasarmu, tare kuma da samar da wannan hidima ga karin kasashen duniya."

A cikin shekarar da ta gabata, kasar Sin ta kuma hada kanta da kasashe da dama da suka hada da Faransa da Italiya da Brazil ta fannin tauraron dan Adam.
A watan Oktoban bara a cibiyar harba tauraron dan Adam na Jiuquan ta kasar Sin, an harba tauraron dan Adam da aka kera bisa hadin kan kasashen Sin da Faransa, wanda zai samar da bayanan da ya samu ga masanan ilmin kimiyya na kasashen biyu duka, matakin da zai fadada hadin gwiwar kasashen biyu ta fannin binciken fasahohin sararin samaniya da na teku. A game da wannan, Patrik Castillan, manajan kula da ayyukan wannan tauraro daga bangaren Faransa ya ce, wannan hadin gwiwa ce ta cin moriyar juna. Ya ce,"Mun cimma daidaito a fannoni da dama, mun kuma gyara wasu ayyukan da muka saba gudanarwa a yayin da muke yin koyi da juna. Misali idan bangaren Faransa na ganin wasu dabaru ko ma'aunai na kasar Sin sun fi namu, to za mu gyara namu, haka ma takwarorinmu na kasar Sin suke. Abin da nake son jaddadawa shi ne, wannan hadin gwiwa ne na cin moriyar juna, kuma dukkanmu mun amfana da hadin gwiwar." (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China