Ofishin shugaban kasar Iraki ya bayar da sanarwa a wannan rana cewa, shugaban kasar Barham Salih ya bayyana a yayin ganawarsa tare da Pompeo cewa, yana son kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa da yankuna, da kawar da rashin tabbaci a yankin Larabawa, da warware matsalar ta'addanci da tsattsauran ra'ayi. A nasa bangare, Pompeo ya bayyana cewa, kasar Iraki muhimmiyar abokiyar kasar Amurka ce a fannonin siyasa da tattalin arziki da tsaro, kasar Amurka tana son zuba jari da shiga aikin sake gina kasar Iraki, musamman taimakawa wajen sake gina biranen da aka karbe ikonsu daga hannun kungiyar IS.
Pompeo ya kuma gana da firaministan kasar Iraki Adel Abdul Mahdi da shugaban majalisar dokokin kasar Mohamed al-Halbousi da kuma ministan harkokin wajen kasar Muhammad Ali al-Hakim.
Pompeo ya fara kai ziyara a kasashe 8 na yankin Gabas ta Tsakiya ciki har da kasar Jordan, da Masar, da Saudiyya tun daga ranar 8 ga wannan wata. Bisa shirin kai ziyara da aka tsara, bai kunshi kasar Iraki ba. Majalisar gudanarwar kasar Amurka ta bayyana a ranar 4 ga wata cewa, a yayin ziyarar Pompeo, za a yi alkawari ga kasashen kawacenta cewa, kasar Amurka ba za ta janye daga yankin Gabas ta Tsakiya ba domin tinkarar barazanar kasar Iran tare da su. (Zainab)