Gwamnatin kasar Yemen da 'yan tawayen Houthi sun nuna cikakkiyar mutuntawa ga yarjejeniyar tsakaita bude wuta a birnin Hodeidah na kasar, in ji Martin Griffiths, wakilin musamma na MDD kan batun Yemen, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba.
"Ina farin cikin sanar da cewa, dukkan bangarorin sun amince da yarjejeniyar tsakaita bude wutar a Hodeidah, wacce aka amince za ta fara aiki tun a ranar 18 ga watan Disamba, kuma an samu gagarumin ci gaba wajen raguwar tashe tashen hankula tun daga wancen lokaci," Griffiths ya bayyana hakan ne ga kwamitin sulhun MDD.
Ana samun tashe tashen hankula a wasu yankuna, da suka hada da birnin Hodeidah, da kuma wasu yankunan kudancin kasar Yemen. Sai dai kuma, tashe tashen hankula ba su da yawa sosai idan an kwatanta da gabanin lokacin kulla yarjejeniyar a kasar Sweden, in ji shi.(Ahmad Fagam)