in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama 'yan kasar Habasha 171 bisa zarginsu da hannu a rikicin kabilanci
2019-01-10 10:15:00 cri

Gwamnatin kasar Habasha ta sanar a jiya Laraba cewa, ta kama mutane 171 wadanda take zarginsu da hannu wajen haddasa rikicin kabilanci a yammacin kasar.

Kasar Habasha ta kafa wata rundunar tsaron musamman da nufin tabbatar da zaman lafiya a yankunan kan iyakokin kasar a jihohin Benishangul Gumuz da Oromia dake fama da tashin hankali, an cafke mutanen ne a 'yan kwanakin da suka gabata, kamar yadda kafar yada labarai mallakar gwamnatin kasar ta ba da rahoto.

A watan Disamba, kasar Habasha ta kafa rundunar tsaron musamman domin magance matsalolin tsaro a yankunan Benishangul Gumuz da Oromia.

Matakin kafa rundunar tsaron ya zo ne kwanaki kadan bayan hallaka fararen hula 10 a sanadiyyar fashewar wata nakiya da aka binne a karkashin kasa a yammacin jihar Benishangul Gumuz.

Yankunan kan iyakoki biyu, na fuskantar yawan tashe tashen hankula a 'yan shekarun nan, inda aka samu hasarar rayuka a sanadiyyar fadan wanda ya shafi kungiyoyin kabilu daban daban dake zaune a yankunan kan iyakokin. Tashin hankalin ya samo asali ne sakamakon kaddama kan mallakar gonaki da kuma albarkatun kasa dake yankin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China