in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin da aka yi a Gabon
2019-01-09 09:12:05 cri

Shugaba Muhammadu Buharin na Najeriya ya yi Allah wadai da yunkurin da wasu sojoji suka yi na kifar da gwamnati a kasar Gabon a ranar Litinin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Buhari ya yi kira da a mutunta tsarin demokiradiya da ma tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar mai arzikin mai dake tsakiyar Afirka.

Buhari ya ce, zamanin juyin mulkin soja a gwamnatocin Afirka da ma duniya baki daya ya zama tsohon yayi, don haka ya bukaci jami'an sojojin dake da burin shiga harkokin siyasa da su tube bakinsu ko kuma su mayar da hankali kan aikin da kundin tsarin mulki ya zana musu. Ya kuma yi kira ga 'yan kasar Gabon da su goyi bayan bangaren zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro da ma tsarin demokiradiya a kasarsu.

A ranar Litinin din ce kuma, fadar shugaban kasar Gabon ta sanar da damke madugun sojoji 'yan tawayen da ya jagoranci yuyin mulkin na ranar Litinin da bai yi nasara ba a kasar, inda aka kashe biyu daga cikin sojojin bayan da suka shiga tashar gidan radiyon gwamnati, inda suka sanar da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Yanzu haka dai shugaba Ali Bango na Gabon yana farfadowa a wani asibiti a kasar Morocco, bayan matsalar shanyewar gyefen jikinsa da ya gamu da ita a farkon watan Oktoban shekarar 2018 da ta gabata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China