in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in CPC ya gana da babban sakataren jam'iyyar FRELIMO ta Mozambique
2019-01-08 14:21:33 cri

A yau ne mamban hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS Huang Kunming ya gana da babban sakataren jam'iyyar Mozambique Liberation Front (FRELIMO) Roque Silva Samuel a birnin Beijing.

Huang wanda har ila shi ne shugaban sashen fadakar da jama'a na kwamitin kolin JKS, ya bayyana fatan cewa, JKS da FRELIMO za su yi aiki tare don aiwatar da muhimmin matsayin da shugabannin kasashen biyu suka cimma da inganta musaya tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, ta yadda za su daga matsayin alakar dake tsakanin jam'iyyun da ma kasashen biyu zuwa wani sabon mataki.

A nasa jawabin, Silva ya bayyana cewa, jam'iyyarsa ta yaba dangantakar abokantaka dake tsakanin jam'iyyarsa da JKS kana a shirye jam'iyyarsa take ta yi koyi da kwarewar JKS wajen kara karfafa alakar kasashensu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China