in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin kasar Gabon da ba a cimma nasara ba
2019-01-08 10:54:08 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi Allah wadai da yunkurin hambarar da shugaban kasar Gabon Ali Bongo wanda yake kokarin farfadowa daga matsalar shanyewar jiki da ya fama da ita a kasar Morocco.

Kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya bayyana cewa, an yiwa babban sakataren MDD da sauran bangarori bayani game da yunkurin juyin mulkin da aka yi a Libreville,babban birnin kasar. Wakilin musamman na MDD mai kula da harkokin Afirka ta tsakiya Francois Lounceny Fall yana sa-ido sosai kan batun, kan zai shiga-tsakani idan akwai bukatar hakan.

Kakakin ya kara da cewa, babban sakataren MDD ba ya goyon bayan juyin mulki musamman juyin mulki ta hanyar amfani da karfin tuwo. Don haka ya yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin kasar Gabon na ranar Litinin da safe da bai yi nasara ba.

Babban sakataren MDD ya gano cewa, yanzu haka al'amura sun daidaita a birnin Libreville, kana ya yi kira ga masu yunkurin juyin mulki da su bi kundin tsarin mulkin kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China