in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Houthi: Sun tattauna da manzon musamman na MDD kan batun tsagaita bude wuta
2019-01-08 10:39:40 cri

Jiya Litinin manzon musamman na MDD kan batun Yemen Martin Griffiths ya bar kasar, daga baya dakarun Houthi dake kasar sun bayyana cewa, sun tattauna kan batun tsagaita bude wuta a birnin Hudaydah na kasar da sauransu.

Wannan rana, Griffiths ya tashi daga kasar ta Yemen daga filin saukar jiragen saman Sana'a, fadar mulkin kasar. Dakarun Houthi na kasar sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na SABA cewa, yayin ziyararsa a kasar, Griffiths ya sha ganawa da jagoran dakarun Abdul Malik Houthi da kuma shugaban hukumar koli ta juyin juya hali ta dakarun Mohammed Ali al-Houthi, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yadda za a tabbatar da yarjejeniyar tsagaita bude wutar da gwamnatin Yemen da dakarun Houthi suka daddale.

Kana sassan biyu sun yi musanyar ra'ayoyi kan yadda za a gudanar da wani sabon zagaye na shawarwarin shimfida zaman lafiya a kasar ta Yemen da bude filin saukar jiragen saman Sana'a da samar da taimakon jin kai a kasar da sauransu.

A nasa bangare, shugaban hukumar koli ta juyin juya hali ta dakarun Houthi Mohammed Ali al-Houthi ya wallafa wani bayani a dandalin sada zumunta a ranar 6 ga wata, inda ya bayyana cewa, kawo yanzu sassan biyu ba su tabbatar da lokaci da kuma wurin da za su gudanar da shawarwari ba, kana ya bukaci a bude filin saukar jiragen saman Sana'a tare kuma da cire katangar da aka sanya a yankunan da dakarunsa suka mamaye.

A ranar 5 ga wata ne dai manzon musamman na MDD Griffiths ya sauka a Sana'a, fadar mulkin kasar Yemen, an kuma ce zai je Riyadh, fadar mulkin kasar Saudi Arabiya domin ganawa da shugaban Yemen Abdurabbuh Mansur Hadi a can.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China