in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in CPC: Ya kamata a kara yayata manufofi karkashin jagorancin tunanin Xi
2019-01-08 10:31:30 cri

Zaunannen mamba a hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS, kana mamba a sakatariyar kwamitin kolin JKS Wang Huning ya yi kira da a inganta aikin yayata manufofin kasa karkashin jagorancin tunanin Xi Jinping kan tsarin gurguzu na mai sigar musamman na kasar Sin a sabon zamani da ake ciki.

Jami'in wanda ya bayyana hakan yayin taron manyan jami'an fadakar da jama'a na kasar. Ya kuma zayyana muhimmancin cimma nasarar fadakar da jama'a da aikin yayata manufofi, ta yadda za a kara gina JKS da ma kasar baki daya.

Ya ce, ya kamata aikin fadakar da jama'a na wannan shekara, ya mayar da hankali kan taken bikin cika shekaru 70 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, don zaburar da jama'a su kasance masu aiki tukuru.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China