in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan sabuwar kirar da aka yi a kasar Sin a shekarar 2018 ya kai miliyan 1.602
2019-01-07 19:13:03 cri

Darektan hukumar dake kula da hakkin mallakar kira ta kasar Sin, Shen Changyu, ya ce yawan sabuwar kirar da Sinawa suka yi a bara ya kai miliyan 1 da dubu 602, adadin da ya karu da kashi 18.1% bisa na shekarar 2017.

Jami'in ya bayyana hakan ne a yau Litinin a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, yana mai cewa, kasar Sin za ta kara kokarin kare hakkin mallakar kira a bana. Kaza lika kasar za ta tsara cikakken shirin raya harkar kare hakkin mallakar kira, da kafa manufofi masu alaka da aikin, gami da shirin kafa wata cibiyar aikin kare hakkin mallakar kira. A sa'i daya kuma, kasar za ta zurfafa hadin gwiwarta da sauran kasashe a wannan fanni, in ji jami'in. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China