Cikin wata sanarwar da wani jami'in rundunar ya karanta ta kafar Radiyon kasar, sojojin sun zargi shugaban kasar Ali Bongo Ondimba, wanda a yanzu yake jinya a wani asibitin dake kasar Morocco, da gazawa wajen sauke nauyin dake kansa na shugabanci, suna masu cewa, bayanin da ya gabatar domin murnar shiga sabuwar shekara, a ranar 31 ga watan Disambar da ya shude, cike yake da farfaganda ta yunkurin ci gaba da rike madafun iko.
Shugaba Bongo ne shugaban Gabon tun daga shekarar 2009, an kuma sake zabensa a karon karshe a shekarar 2016.
Rahotanni na cewa, sojojin sun shiga farfajiyar gidan radiyon kasar ne da misalin karfe 4 na asubahin Litinin din nan bisa agogon kasar. (Saminu Hassan)